Gwamnatin jihar Legas ta ce za ta rufe makarantun da suka kasa bin umarnin gwamnati na komawa makaranta a ranar 4 ga watan Disamabar 2022.
Darakta Janar na ofishin tabbatar da ingancin ilimi, Abiola Seriki-Ayeni ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar.
Gwamnatin ta ce a na tattara sunayen makarantun da su ka gaza bin umarnin ma’aikatar ilimi ta jihar na cewa su koma makarantu masu zaman kansu da na gwamnati a ranar Talata 4 ga watan Janairu 2022, kuma za a dauki matakin ladabtarwa nan ba da jimawa ba.
Ta kuma ce, samar da kalandar makaranta da ta dace tare da masu ruwa da tsaki a fannin ilimi da tabbatar da bin doka da oda, inda ta jaddada cewa aikin sa ido da jami’an hukumar suka fara shi ne na tantance matakin da a ka dauka a fannin ilimi.
Da ya ke bayyana cewa wasu makarantu sun ki bin umarnin, da ya bayyana cewa an samar da jadawalin da ta dace da makarantu na 2021/2022 tare da masu ruwa da tsaki a watan Yunin 2021 domin tabbatar da daidaito a tsarin ilimi.
Ta ce an sanar da yarjejeniyar ga dukkan makarantu da kungiyoyi ,domin tabbatar da daidaiton matakan ilimi da tsarin koyo.