fidelitybank

Za mu mamaye Kano da bishiyu – Gidauniyar Panacea Foundation

Date:

Gidauniyar Panacea Foundation mai zaman kanta a Kano, ta ce za ta dasa bishiyu 100,000 a makarantun Kano da al’umma a shekarar 2022.

Wanda ya kafa kungiyar, Dahir Hashim, ya zanta da kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ranar Talata a Kano.

Hashim ya ce, an yi aikin ne da nufin dakile matsalar zafi a Kano.

“Za mu mai da hankali kan shuka a makarantu ta yadda dalibai za su samu damar sanin kansu da dashen itatuwa da kuma kula da su,” in ji shi.

A cewar Hashim, manufar dashen bishiyar ita ce yin tasiri ga dimbin sake koren garin Kano.

“A shekarar 2021, mun dasa bishiyoyi sama da 10,000 a makarantu da al’ummomi daban-daban a cikin kananan hukumomin Kano.

“A wannan lokacin, mun shirya gangamin wayar da kan jama’a, domin wayar da kan muhalli tsakanin yaran makaranta, al’ummomi, da ofisoshin gwamnati,” in ji shi.

Hashim ya ce, gidauniyar ta kuma horas da kungiyoyi masu zaman kansu kan yadda za su kula da bishiyun da kuma yadda za a rika samar musu da taki na gida.

Ya ce gidauniyar ta na da ‘yan agaji da s uka yi aiki a matsayin masu kula da kowace karamar hukuma a fadin jihar.

Hashim ya ce “Muna yin wadannan duka ne domin ganin an kula da itatuwan da mu ka dasa sosai kuma dukkansu za su tsiro domin amfanin al’umma.”

Ya kara da cewa aikin shine domin inganta rayuwar al’umma gaba daya a Kano.

Hashim ya roki goyon bayan jama’a wajen ganin Kano ta zama koraye, domin kare birnin daga sauyin yanayi.

 

spw news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp