Ma’aikatar ilimi a jihar Zamfara ta sanar da sake bude makarantu a yau Litinin.
Cikin wata sanarwa da ma’aikatar da fitar cewa, za a bude makarantun firamare da na sakandire a ranar 17 ga watan Janairun 2022.
Sanarwar ta ce, makarantun gaba sakandire kuma za su kasance a rufe har sai yanayin tsaro ya inganta.
A watannin baya ne aka rufe makarantun jihar, saboda matsalolin tsaron da ake ci gaba da fuskanta ciki har da satar dalibai.