fidelitybank

Za a rufe filin jirgin saman Legas

Date:

Daga ranar 1 ga watan Oktoban shekara ta 2023, za a rufe filin jirgin sauka da tashin jiragen saman Murtala Muhammed da ke Legas, bayan wani matakin yin wasu gyare-gyare da za a yi a harabar filin jirgin da aka kwashe kusan shekara 43 da ginawa.

Ministan ma’aikatar lura da sufurin jiragen saman Najeriya, Festus Keyamo ne ya bayyana hakan, inda ya shawarci kamfanonin jiragen sama na Æ™asashen waje da su yi amfani da sabuwar harabar da aka kammala kafin a kammala aikin.

Wannan dai ana ganin zai shafi sha’anin sufurin jiragen sama a filin jirgin matuÆ™ar ba an kammala aikin da wuri ba.

A watan Maris ɗin shekara ta 2022 tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ƙaddamar da buɗe sabon aikin gyaran filin jiragin, amma aikin na fuskantar tafiyar hawainiya.

A shekrar 2019, tsohon ministan sufurin jirgen sama Hadi Sirika ya fito da shirin rufe filin jirgin saman, sakamakon mummunar lalacewar da ya yi, amma ba a samu damar aiwatar da hakan ba.

Haka ministan ya bayar da sanarwar dakatar da shirin samar da kamfanin jirgin saman Najeriya har sai ya tattauna da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.

Festus Kiyamo ya bayyana cewa za a É—auki matakan gaggawa da suka haÉ—a da siyo motocin safa-safa domin É—aukar fasinjoji a filin jirgin.

Ya ce babban abin damuwa ga ‘yan Najeriya da baÆ™i shi ne yanayin filin jirgi, abin da ya sa za a yi amfani da sabon da wani kamfanin Æ™asar Chana ya gina.

daily sun news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp