fidelitybank

Za a fara kai Shinkafar Najeriya zuwa Jamhuriyar Benin

Date:

Gwamnatin kasar Benin ta amince ta bai wa daya daga cikin manyan kamfanonin sarrafa shinkafa a Najeriya, Labana Rice Mill, eka 30,000 na filin noman shinkafa a cikin kasarta domin nomanta a can.

Wannan wani bangare ne na wata yarjejeniya da aka kulla tsakanin kamfanin na Labana da gwamnatin makwabciyar Najeriya.

BBC ta rawaito cewa, hukumomin aikin gona na kasar sun ce Benin na da filayen noma da suka dace da noman shinkafa har eka 360,000 amma kashi 10 cikin 100 na filayen ne kawai ake noma a cikinsu.

An kulla yarjejeniyar ce a karshen mako bayan musayar ziyara tsakanin jami’an kamfanin da kuma na lamurran ayyukan gona na jamhuriyar ta Benin.

Kamfanin na Labana ya ce manufarsa ta shiga yarjejeniyar ita ce faÉ—aÉ—a kafofin da ya ke samun shinkafa shanshera a kokarin da ya ke na fadada yawan shinkafar da ya ke samarwar daga ton 16,000 a kowace awa daya zuwa 40,000, abin da ya ce zai sa ya zamo kamfanin shinkafa mafi girma a yammacin Afrika.

A nata bangaren, gwamnatin Benin ta kulla yarjejeniyar ce, domin cimma muradin shugaban kasar na habbaka noman shinkafa.

uanguard news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

An sake mayar da yan Najeriya 294 gida daga Nijar

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Najeriya Nema ta...

An gano motoci 35 da aka sace a wata shida

Hukumar kiyaye haɗurra ta ƙasa a Najeriya ta ce...

Shugaban Laberiya ya je ta’aziyyar Buhari a Monrovia

Shugaban Ƙsaar Laberiya Joseph Nyuma Boakai ya kai ziyarar...

Rundunar Yansandan Kaduna ta hana gangamin goyon bayan Peter Obi

Rundunar 'yansandan Najeriya reshen jihar Kaduna ta hana gudanar...

Iran ta zartar da hukuncin kisa a kan Mutane 3

Hukumomi a Iran sun zartar wa mutum uku hukuncin...

Ƴansanda sun kama ƙasurgumin ɗanbindiga a Kaduna

Rundunar Æ´ansandan jihar Kaduna ta ce, jami'an ta sun...

Sudan ta Kudu ta yi ta’aziyyar Buhari

Mukaddashin Ministan Harkokin Wajen Sudan ta Kudu, Ambasada Akuei...

Trump ya na fama da cuta mai kumbura kafa da toshewar hanyar jini

A ranar Alhamis ne Fadar White House ta sanar...

Yadda aka gudanar da addu’o’in Buhari a Villa

A ranar Alhamis ne aka gudanar da addu'o'i ga...

Rasha tarnaki ce a wajen Tarayyar Turai – Jamus

Shugaban gwamnatin Jamus Friedrich Merz ya shaidawa BBC cewa...

Amurka ba ta goyon bayan Isra’ila a harin Syria – Trump

Amurka ta ce ba ta goyon bayan hare-haren da...

Tinubu zai zo Kano ta’aziyyar Dantata

Shugaban Najeriya, Bola Tinubu zai kai ziyara Kano yau...
X whatsapp