fidelitybank

Yarjejeniyar tsagaita wuta ta fara aiki tsakanin Hamas da Isra’ila

Date:

A daidai ƙarfe 9:15 agogon GMT yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra’ila da Hamas ta fara aiki a Gaza.

Hakan na nufin yaƙin da ak ƙwamawa tsakanin dakarun Isra’ila nda na Hamas zai tsaya sannan kuma za a saki mutanen da Hamas ke garkuwa da su ƴan Isra’ila sannan ita kuma Isra’ila ta saki Falasdinawa da ke gidajen yarinta.

Da farko dai tsagaita wutar ta ɗan samu cikas a safiyar ranar Lahadi bisa abin da Isra’ila ta ce sai Hamas ta fitar da jerin sunayen mutanen da ke hannuta waɗanda za a saki sannan yarjejeniyar ta fara aiki.

Daga bisani ne kuma Hamas a shafinta na X ta saki jerin sunayen wasu mata uku da ta ce na cikin waɗanda za ta saki a zangon farko.

Ita kuma Isra’ila ta fitar da jerin nata na mutum 33 da ta ce su ne take sa ran za su kasance a zangon farko da suka haɗa da wanda ya fi kowanne ƙarancin shekaru.

Ministan tsaron Isra’ilar dai, Itamar Ben-Gvir ya yi murabus daga kujerarsa bisa abin da ya ce miƙa wa Hamas nasara ce. In ji BBC.

breaking news in nigeria today punch

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp