fidelitybank

Yanzu-Yanzu: A na ci gaba da sauraron shaidu a kan shari’ar Abduljabar da gwamnati

Date:

A safiyar yau Alhamis an ci gaba da saurarenshari’ar Sheikh Abduljabbar da gwamnatin jihar Kano, a kan shari’ar da a ka fara gabatar wa tun shekarar da ta gabata, bisa zargin kalaman ɓatanci da kuma tunzuri.

Kamar yadda ya gabata, a zaman na yau zai ɗora ne da shedu 4 da masu gabatar da ƙara suka kawo gaban kotu, Farfesa Ahmad Murtala wanda ya zo kotu a matsayin masani kuma kwararre a ilimin hadisi.

A zaman na yau, Lauyoyin masu gabatar da kara karkashin jagorancin, Barista Sa’ida Shu’aibu SAN, sun fara da gabatar da kansu, sannan ya bada damar ci gaba da gabatar da jawabi ga Fafesa Usman Shu’aibu. Sun gabatar wa da kotu shedar kammala digirin farko, na biyu da na uku a kotu, sannan kuma an gabatar da shedar kasancewar shedar Farfesa a jami’ar Bayero dake Kano, da kuma shedar zaman da shugaban sashen Addinin Musulunci na jami’ar Bayero dake Kano.

Shedar ya kuma gabatar da Ijazozin sa ga kotu har guda shida.

”Silsila ce har zuwa manyan littafan hadisai guda 6, da kuma sauran littafan hadisai sanannu, sannan suna bani damar na ruwiaci waɗannan hadisai zuwa Annabi SAW, suna kuma bani damar na karantar dasu na fassara” inji Sheda Farfesa Ahmad Murtala

Bayan gabatar da wadannan takardu na shedar a gaban kotu, kotu ta karɓe su a matsayin sheda abar nuni a cikin Shari’a, inda tayi musu lamba da (Exhibit D, E , F, G, H, I, J1-J6).

Lauyan masu gabatar da kara sun nemi shedar da ya sake fassara hadisan sannan kuma kotu ta shigar da fassarar cikin jawabin da take rubutawa akan shari’ar.

Shedar ya fassara hadisan a kotu, sannan alƙali ya bada hutun minti 30 dan wanda ake ƙara Malam Abdujabbar yayi nazari akai kafin ya yi tambayoyin sa ga shedar. Za a koma shari’ar da misalin karfe 12:00 na rana.

naija news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp