fidelitybank

‘Yan zanga-zanga sun lalata kadarori na Biliyan 5 – Gwamnatin Jigawa

Date:

Gwamnatin jihar Jigawa ta bayyana cewa an lalata kadarori na Naira biliyan 5 a zanga-zangar da aka yi a fadin kasar a watan Agustan 2024.

Shugaban kwamitin tantance masu zanga-zangar Bello Fanini ne ya bayyana hakan a lokacin da yake gabatar da rahoton kwamitin ga gwamna Umar Namadi a fadar gwamnati dake Dutse babban birnin jihar.

Fanini, ya bayyana cewa kadarorin da aka lalata sun hada da na gwamnatin tarayya, jiha, da kananan hukumomi, da kuma wasu mutane masu zaman kansu da kuma ‘yan kasuwa.

Da yake warware asarar da aka yi, ya ce, “Gwamnatin Jihar Jigawa ta yi asarar da ta kai Naira biliyan 2.8, yayin da Gwamnatin Tarayya da hukumominta suka yi asarar Naira biliyan 1.07. Masu zaman kansu da kamfanoni sun yi asarar ₦707 miliyan, kananan hukumomi sun yi asarar da suka kai miliyan 364, sannan jam’iyyar All Progressives Congress, APC, ta yi asarar sama da miliyan 49.”

Kwamitin ya kuma bayar da shawarwari da dama da nufin hana afkuwar irin haka nan gaba. Daga cikin muhimman shawarwarin akwai bukatar gwamnatin jihar ta biya kamfanoni da daidaikun mutane da suka yi asarar dukiyoyi yayin zanga-zangar.

Da yake mayar da martani, Gwamna Umar Namadi ya nuna jin dadinsa ga kwamitin bisa sadaukarwar da suka yi tare da ba su tabbacin cewa gwamnati za ta yi nazari sosai kan rahoton tare da aiwatar da shawarwarin da aka gabatar.

Idan dai ba a manta ba Gwamna Namadi ne ya kaddamar da kwamitin binciken da zai binciki musabbabin zanga-zangar da aka yi a jihar Jigawa a ranar 1 ga watan Agustan 2024.

thisday newspaper

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp