Wasu ‘yan ta’adda sun yi garkuwa da mutane 11, ciki har da babban limami, Aminu Garba, wanda ke shirin gabatar da sallar Juma’a a kauyen Gatawa da ke karamar hukumar Sabon Birni a jihar Sokoto.
Lamarin dai ya faru ne a ranar Juma’a inda a ka yi garkuwa da limamin tare da wasu mutane uku.
Maharan sun kuma tare hanyar Sabon Birni zuwa Gatawa a ranar Asabar, inda suka harbe mutane uku tare da yin garkuwa da wasu bakwai.
Dan majalisar mai wakiltar mazabar Sabon Birni ta Kudu a majalisar dokokin jihar, Sa’idu Ibrahim, wanda ya tabbatar da harin, ya ce”Wadanda suka jikkata a halin yanzu suna karbar kulawa a wani asibiti da ke Wamakko”.