fidelitybank

‘Yan sanda sun kama likitan Bello Turji shugaban ‘yan ta’adda a Sokoto

Date:

Rundunar ‘yan sandan jihar Sokoto ta kama wani ma’aikacin lafiya, Abubakar Hashimu, wanda ya yi wa fitaccen shugaban ‘yan bindigan da ya addabi yankin, Bello Turji, magani a lokacin da sojoji suka raunata shi a wani hari da suka kai shekaru uku da suka wuce.

Da yake jawabi ga manema labarai a ranar Litinin, Mataimakin Sufeto Janar na ‘yan sanda na ayyuka, Ahmed Zaki, ya ce, an kama Hashim ne tare da wasu 36.

Wasu daga cikin wadanda ake zargin sun hada da Musa Kamarawa, Bammi Kiruwa, Zayyanu Abdullahi, Hardo Yunusa da Samuel Chinedu, da dai sauransu.

A cewar sa, an kama mutanen ne tsakanin 20 ga watan Janairu zuwa 29 ga watan Janairu, bayan da rundunar ‘yan sandan Najeriya ta Operation Sahara Storm ta gano tare da kai sumame sansanonin ‘yan bindigar da ke kananan hukumomin Illela, Rabah, Isa da Goronyo a jihar Sakkwato.

Rundunar ‘yan sandan ta kuma ce, an kama shi ne a wani dakin otel da ke cikin birnin Sakoto, a lokacin da yake jiran kudinsa bayan ya baiwa ‘yan bindigar magunguna da sauran kayan masarufi.

legit.news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp