fidelitybank

‘Yan sanda sun gayyaci tsohon kwamishinan gwamnatin Ganduje

Date:

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano, ta gayyaci tsohon kwamishinan ayyuka a gwamnatin gwamna Abdullahi Umar Ganduje, Muazu Magaji.

Da ya ke zantawa da Aminiya, Magaji ya ce, ofishin siyasa na hukumar SBI ne ya gayyace shi, amma ba su bayyana masa mene ne makasudin gayyatar ba.

“Na sami waya cewa suna son in bayyana a gabansu. Na tambaye su a kan menene ? kuma suka ce min zan san duk abubuwan da ke faruwa idan na zo.

“Lokacin da na je sai suka ce, gwamnatin jihar Kano ce ta kai kara ta,” inji shi.Da aka tambaye shi ko ya mutunta gayyatar? Tsohon kwamishinan ya ce, “A yanzu haka ina Abuja, kuma zan mutunta gayyatar da zarar na isa Kano a ranar Talata.

“Me nake gudu? Tabbas zan girmama gayyatar gobe,” ya tabbatar.

Sai dai jami’in hulda da jama’a na rundunar, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa bai samu, cewa uffan ba game da lamarin.

Magaji dai ya sha cece-kuce tun bayan da aka kore shi daga mukamin kwamishinan ayyuka.

Gwamnan ya sa ke nada shi a matsayin mai taimaka masa kan bututun iskar gas na AKK, amma ya kore shi daga baya.

Tun daga wancan lokacin tsohon kwamishinan da aka kora ya rinka sukar Ganduje da gwamnatinsa a Facebook.

A halin yanzu, Magaji dan tsagin Shekarau ne na jam’iyyar APC.

www.punch news.ng

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp