‘Yan sanda a kasar Tunisiya sun tarwatsa masu zanga-zanga sama da 1,000 da ke kokarin isa tsakiyar birnin Tunis.
Masu zanga-zangar na nuna adawa da shugaban kasar na nuna rashin amincewa da takunkumin Korona.
Ma’aikatar harkokin cikin gida ta kasar ta ce mutane 1,200 ne suka yi zanga-zangar kuma ta ce dakarunta sun yi taka-tsantsan.
Kasancewar ‘yan sanda da yawa ya hana masu zanga-zanga da dama yin taro a titin Habib Bourguiba, babban titin tsakiyar Tunis wanda shi ne wurin da aka saba gudanar da zanga-zangar ciki har da lokacin juyin juya halin na 2011 wanda ya kawo sauyin dimokiradiyyar kasar.