Wasu ’yan daba sun kai hari tare da kona shelkwatar karamar hukumar Ezza ta Arewa a jihar Ebonyi, gabanin zabe mai zuwa.
Rahotanni sun nuna cewa, hare-haren da kona karamar hukumar Ezza ta Arewa, ya zo ne daf da rantsar da sabon shugaban karamar hukumar a jihar.
Ku tuna cewa Nora Alo, tsohon shugaban karamar hukumar Ezza ta Arewa kuma ya mika wa sabon shugaban Mista Ogodo Ali Nomeh.
An tattaro cewa barayin sun kutsa cikin wasu ofisoshi, inda aka ajiye muhimman takardu suka kwashe su tare da kona wasu daga cikinsu.
Da yake tabbatar da faruwar harin, sabon shugaban karamar hukumar, Mista Ogodo Ali Nomeh, ya ce ‘yan ta’addan sun yi artabu da jami’an tsaron da ke kula da majalisar ne, kuma wasu daga cikin ‘yan bindigar sun samu raunuka a harbin bindiga.
Ya ce har yanzu ba a kama ‘yan ta’addan ba har zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto.
A cewarsa: “Ba mu kama kowa ba a yanzu. Kun san abin ya faru da daddare kuma kafin mu fito da safen nan tuni suka tsere.
“Akwai harbin bindiga da yawa. Kuma ina tsammanin da yawa daga cikinsu sun ji rauni. Don haka, muna tafiya daga wannan asibiti zuwa wancan don duba mutanen da suka samu raunukan harbin bindiga.
“Ba mu zargin kowa a yanzu, har sai mun kama wadanda ake zargin. Kun san lamarin ya faru ne da misalin karfe 2:00 na safe.
“Muna tattaunawa da jami’an tsaro da suka yi karo da ‘yan ta’addan,” in ji shi.