Rahotanni sun ce ‘yan bindiga sun kwace iko da wasu yanki a jihar Neja, inda suka kafa kofofin karbar haraji tare da sanya haraji kan manoma da mazauna yankin.
Yankunan da abin ya shafa sun hada da Dogon-Dawa, Kurege, Kangarewa, Mangoro, da sauransu, inda aka ce ‘yan bindigar na gudanar da yankunan ne bisa ka’idojinsu.
Mazauna yankin sun bayyana cewa ‘yan ta’addan sun sanya dokar hana zirga-zirgar kayayyaki da jama’a, lamarin da ya tilasta musu biyan haraji kafin tafiya.
A cewar shaidun gani da ido, a ranar Lahadin da ta gabata, an tilasta wa mazauna yankin biyan harajin Naira miliyan 3.5 kafin a bar motocin da ke dauke da kayansu su bar yankin.
‘Yan fashin dai ba su bar manoman ba, inda suka bukaci a biya su haraji kan amfanin gona da kuma tilasta musu biyan kafin a bar su su girbe amfanin gona.
Lamarin dai ya ta’azzara, har ta kai ga har ’yan gudun hijirar da ke neman ficewa daga yankin su biya takamammen haraji kafin tafiyarsu, kamar yadda shaidan ya yi zargin.
Wata majiya mai tushe ta bayyana cewa ‘yan bindigar sun kirkiro yankin nasu ne, suna gudanar da ayyukansu ba tare da adawa ba.
Rahotanni sun bayyana cewa ana cajin motocin da ke barin yankin tsakanin Naira 200,000 zuwa Naira 300,000, inda aka tilasta wa hadakar motoci uku biyan Naira miliyan daya kafin a bar su su fita.
Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Neja, Wasiu Abiodun domin jin ta bakinsa kan lamarin, ya tabbatar da cewa za a gudanar da bincike, kuma za a yi karin bayani.


