Ƴan bindiga sun kai hari wani sansanin sojoji a kauyen Nahuta da ke jihar Katsina, inda suka fatattaki sojoji da cinna wa motocinsu wuta.
Sun kuma kutsa cikin shaguna da gidajen mutane tare da sace kayan abinci da dabbobi da kuɗinsu ya kai miliyoyin naira, a cewar kamfanin dillancin labarai na Reuters.
Wani mazaunin kauyen Isa Bello, ya faɗa wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa harin kan sansanin sojin wanda ke ɗauke da sojoji, ƴan sanda da kuma wasu jami’an tsaro a karamar hukumar Batsari na jihar ta Katsina, ya faru ne ranar Lahadi.
Sai dai mai magana da yawun ƴan sandan jihar Abubakar Sadiq bai mayar da martani ba da aka tuntuɓe shi don ji daga ɓangarensu.
Gungun ƴan bindiga rike da makamai suna ta cin karensu ba babbaka a faɗin arewacin Najeriya a cikin shekaru uku da suka gabata, inda suka yi garkuwa da ɗimbin mutane, da kashe ɗaruruwa da kuma saka wa mutane fargabar ƙasa tafiya ta hanya ko zuwa gonaki a wasu yankuna.
Bello ya faɗa wa Reuters cewa ƴan bindigar waɗanda suka zo kan babura da kuma wata babbar mota da misalin karfe 10 na dare, sun ci karfin sojojin inda suka shafe sa’o’i uku suna musayar wuta da juna.
Wani jami’in gwamnatin jihar Katsina ya tabbatar da cewa ba a samu asarar rayuka ba a kauyen, in ji Reuters.
Harin ya sanya fargaba a cikin mazauna kauyen na Nahuta, inda yawanci daga cikinsu suka tsere zuwa kauyuka da ke kusa domin neman mafaka.


