Gwamna Nyesom Wike ya zargi shugaban kasa Muhammadu Buhari da tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi da yin katsalandan a zaben gwamna na 2019 a jihar Ribas.
Gwamna Wike ya yi wannan ikirarin ne a ranar Larabar, yayin bikin kaddamar da aikin gina titunan cikin gida a garin Igwuruta da ke karamar hukumar Ikwerre ta jihar.
Ya ce shugaban kasar ta bakin tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi ya yi amfani da jami’an tsaro wajen yunkurin murde zaben gwamna.
Gwamnan ya ce al’ummar jihar sun yi watsi da matakin da hukumomin tsaro suka dauka.
Ya ce “Na ji Mista shugaban kasa ya fada jiya cewa, ba zai tsoma baki ba (a zaben 2023). Ya shaida wa gwamnonin ba zai tsoma baki ba.
“A daya (2019) kun tsoma baki tare da turo mutane su zo su karasa mu a jihar Ribas.
“Na gode shugaban kasa da cewa ba za ku tsoma baki ko tsoratar da kowa ba. Ma’ana babu wata hanya ga jam’iyyar ku.
“Tabbas ya tsoma baki a karon karshe ta hanyar amfani da sojoji ta hannun tsohon ministan sufuri amma jama’a suka tashi suka ce a’a hakan ba zai faru ba.
“Na gode wa shugaban kasa da ya ke son barin gadon gudanar da zabe na gaskiya da adalci”.


