fidelitybank

Waɗanda ke adawa da Trump sun yi zanga-zanga a Amurka

Date:

Dubban masu zanga-zanga yawanci mata sun yi tattaki a titunan babban birnin Amurka, Washington DC, domin nuna adawa da Donald Trump, yayin da ake shirin rantsar da shi gobe Litinin a matsayin shugaban ƙasar a wa’adi na biyu.

Ana yin gangamin ne na jama’a ( People’s March) wanda a baya ake masa laƙabi da Women’s March (Gangamin Mata ) kowace shekara tun 2017.

Gamayyar ƙungiyoyi ce daban-daban ta shirya taron da nufin nuna adawa ga tsare-tsare da manufofin Trump, kamar yadda suka bayyana a shafinsu na intanet.

Ƙungiyoyin na da muradu daban-daban da suka haɗa da batun sauyin yanayi da natun baƙi da shige da fice da kuma ‘yancin mata.

Can ma a birnin New York da Seattle an gudanar da zanga-zanga ƙanana don nuna adawa da Trump ɗin.

Babbar zanga-zangar ta Washington da aka yi jiya Asabar ta zo daidai da zuwan shugaban mai jiran-gado, birnin domin halartar taruka daban-daban na shirin bikin rantsar da shi ranar Litinin.

daily post nigeria news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

‘Yan Arewa su dakata da neman mulki har zuwa 2031 – Sakataren Gwamnati

Sakataren gwamnatin tarayya, SGF, George Akume, ya yi kira...

Matatar Dangote ta janye ƙarar da ta shigar kamfanin NNPCL a kotu

Matatar man Dangote ta janye ƙarar da ta shigar...

Ba mu baiwa Obi shawara ya janye daga takara ba – Kungiyar Inyamurai

Kungiyar koli ta al’adun kabilar Igbo, Ohanaeze Ndigbo Worldwide,...

Dole ne APC ta bar mana kujerar mataimakin shugaban kasa – ANPP

Tsagin tsohuwar jam'iyyar All Nigeria Peoples Party wato ANPP...

Gwamna ya nada Sarkin Gusau

Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal ya amince da naɗin...

‘Yan Bindiga sun yi ikirarin kashe Daliban koyon aikin lauya a Benuwai

Ƴanbindiga da suka yi garkuwa da ɗaliban makarantar samun...

Tinubu ya gwangwaje tawagar Super Falcons da ruwan daloli da gidaje a Abuja

Shugaban kasa, Bola Tinubu, ya bai wa ƴan wasan...

Super Falcons ta sauka a Abuja tare da yin zagayen nuna kofi

Tawagar Super Falcons ta Najeriya sun isa Abuja bayan...

Za a fuskanci katsewar wutar lantarki a Legas tsawon kwana 25

Masu amfani da wutar lantarki a jihar Legas na...

‘Yan Najeriya ku daina bayar da bayan katin dan kasar ku – NIMC

Hukumar Kula da shaidar ɗan ƙasa (NIMC), ta bayyana...

Likitoci a Legas sun fara yajin aiki saboda rage musu albashi

Ƙungiyar likitoci ta Legas (Medical Guild), wacce ke ƙarƙashin...

Yan Bindiga sun yi wa Mutane 38 yankan Rago a Zamfara

Ƴanbindiga sun kashe wasu mutum 38 ta hanyar yi...
X whatsapp