Nan da ɗan wani lokaci Hamas za ta saki wasu mata uku daga cikin ‘yan Isra’ila da ta yi garkuwa da su tsawon wata goma sha biyar.
Sakin nasu zai kasance ne a wani mataki na aiwatar da yarjejeniyar dakatar da buɗe wuta a tsakanin Hamas da Isra’ila, wadda aka daɗe ana fatan gani.
Matasan matan uku su ne – Doron Steinbrecher, da Romi Gonen da kuma Emily Damari.
Bayan sakin nasu ne, Hamas ɗin za ta sake sakin wasu ƙarin talatin amma a rukuni-rukuni a tsawon mako shida.
‘Yan sa’o’i kafin fara aiwatar da yarjejeniyar dakatar da buɗe wutar, hukumar kai ɗauki da Hamas ke tafiyarwa a Gaza ta ce Isra’ila ta kashe aƙalla Falasɗinawa 19 a sababbin hare-hare da ta kai Gaza ta sama.