Dan wasan gaban Napoli Victor Osimhen ya koma ƙungiyar Galatasaray ta Turkiyya a matsayin aro.
Dan wasan mai shekara 25 an ta yaɗa cewa zai koma ƙungiyar Chelsea da ke buga Premier Ingila.
Kazalika an riƙa alaƙanta shi da Al-Ahli ta Saudiyya har zuwa ranar Juma’a ranar ƙarshe ta rufe kasuwar musayar ‘yan wasa a Turai.
Sai dai har aka rufe kasuwar duka bai tafi ko wacce ƙungiya ba daga cikinsu.
Dan wasan Najeriyan ya ci kwallo 76 a wasa 133 da ya buga wa Napoli, kuma ya taka muhimmiyar rawa a Nasarar da ta samu ta lashe Serie A a 2022-23, inda ya ci kwallo 26.