Hukumar kula da kwallon kafa ta nahiyar turai UEFA ta tabbatar da sunayen ‘yan wasa uku da za ta zabi gwarzon dan wasa a ranar Juma’a.
Su ne Kevin De Bruyne na Manchester City da ‘yan wasan Real Madrid na Karim Benzema da Thibaut Courtois.
Benzema ne ke kan gaba a yawan cin kwallaye a kakar wasan da ta wuce a gasar zakarun Turai da kwallaye 15, yayin da abokin wasansa Courtois ya ci kwallo tara a ragar Liverpool a wasan karshe.
Madrid ta fitar da De Bruyne da sauran su a wasan kusa da na karshe a gasar.
An tattara jerin sunayen na karshe bayan da kociyoyi da wasu zababbun ‘yan jarida suka kada kuri’a.
A cikin lambar yabo ta masu horarwa, an tantance Carlo Ancelotti na Madrid tare da Jürgen Klopp na Liverpool da Pep Guardiola na Man City.
Za a sanar da wadanda suka yi nasara a ranar 25 ga watan Agusta a Istanbul a fafatawar da za a yi a matakin rukuni na gasar zakarun Turai ta bana.
Jorginho na Chelsea ne ya lashe kyautar a bara bayan ya taimakawa Chelsea da Italiya lashe kofin Turai.


