Tsohon gwamnan jihar Abia, Orji Uzor Kalu ya bayyana irin sana’o’in da ya yi a kasuwanni da dama da kuma yadda ya samu biliyoyin kudade a rayuwar sa.
Kalu, dan majalisar dattawa mai wakiltar yankin Abia ta Arewa kuma bulaliyar majalisar dattawa, mai burin tsayawa takarar shugaban kasa a 2023.
Sanatan, a wata hira da ya yi da gidan talabijin na Arise a ranar Alhamis, ya ce, ya tsunduma cikin harkokin kasuwanci daban-daban, tun daga sayar da manja zuwa fitar da danyen mai da kuma shigo da sukari daga kasashen waje.
Ya ce, ya kuma kasance ya na yin kwangilar samar da kayan aikin sojojin Najeriya da abinci ga sojoji a fagen fama.
Shahararren marubuci Reuben Abati na cikin ma’aikatan gidan talabijin na Arise da suka yi hira da Sanatan.
Mista Kalu ya ce, ya fara jigilar sayar da manja daga Kudu zuwa Arewa, musamman Maiduguri, tun ya na dalibi a jami’ar Maiduguri.
“Lokacin da na je Maiduguri na gano cewa, Manja na da riba sosai a Maiduguri, ba su da shi. Domin haka duk lokacin da na dawo gida hutu zan sayi Manja in koma. Idan na koma wani hutu, zan sayi busasshen kifi in sayar da su. Haka na fara,” in ji Mista Kalu a cikin hirar.
Sanatan ya ce ya yi karo da Ibrahim Babangida da Muhammadu Buhari ne a lokacin da su ke manyan hafsoshin soji, sai dai bai bayyana yadda mutanen biyu da suka mulki Najeriya suka taimaka masa wajen ci gaban harkokin kasuwancinsa ba.
Ya ce“Ina cikin shigo da sukari da shinkafa da yawa a wani lokaci a rayuwarsa, kuma ya kasance babban abokin takara da Aliko Dangote, mutumin da ya fi kowa kudi a Afirka a yau.
“Na kasance daya daga cikin manyan masu shigo da shinkafa da sukari. A gare ni, samun kudi basira ce. Daga nan na fara gina masana’antu a Aba da Ota.” In ji Kalu.
Ko da ya ke bai yi magana game da wannan ba a cikin hirar Arise TV, Mista Kalu ya na da jari a kafafen yada labarai ya mallaki jaridun Sun da Telegraph.