fidelitybank

Tsohon Ministan Kwadago Akwanga ya rasu ya na da shekaru 77

Date:

Allah ya yi wa tsohon Ministan Kwadago, Alhaji Hussaini Zanwa Akwanga rasuwa.

Mataimakin shugaban karamar hukumar Akwanga a jihar Nasarawa, Alhaji Safiyanu Isa wanda ya tabbatar da rasuwar tsohon ministan ya ce “tsohon ministan ya rasu ne a yau Juma’a, a Akwanga”

Alhaji Akwanga, ya na da shekaru 77 a duniya bayan ya sha fama da jinya a yankin sa na Akwanga da ke karamar hukumar Akwanga ta jihar Nasarawa.

Tsohon Ministan, kwararren malami, ya zama minista a shekarar 2003, amma shugaban kasa na wancan lokacin, Olusegun Obasanjo ya kore shi.

A shekarar 2017, an yi garkuwa da tsohon ministan a gonarsa da ke kauyen Kurmin Tagwaye, kusa da Akwanga, amma bayan kwana biyu a ka sake shi bayan ya biya kudin fansa.

Tuni dai a ka yi jana’izarsa kamar yadda addinin Musulunci ya tanada a garinsu na Akwanga.

 

legit.news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...

A sake sabon tsarin shugabancin INEC a Najeriya – Goodluck

Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, ya yi kira da...

Magoya bayan West Ham ku hada kai da Bowen – Potter

Mai horas da West Ham, Graham Potter ya bukaci...

Alhaki na ne kifewar jirgin kasa – Shugaban Hukumar

Shugaban hukumar jiragen ƙasa ta Najeriya (NRC), Kayode Opeifa,...
X whatsapp