fidelitybank

Tsoffin Ɗaliban BUK ƴan shekarar 1992 sun bada tallafin naira miliyan 1 ga ɗalibai

Date:

 

 

Ƙungiyar Tsoffin Ɗaliban Jami’ar Bayero ta Kano, BUK, ƴan shekarar 1992 sun ci alwashin ɗorewa da bada tallafin naira miliyan 1 a kowacce shekara ga ɗalibai ƴan asalin Jihar Kano.

Ƙungiyar ta fara bada wannan tallafi ne sama da shekaru biyar da su ka gabata.

Bayan tallafin karatun, ƙungiyar kuma na bada wasu taimakon ga ɗalibai da ma jami’ar baki ɗaya a duk lokacin da ta ke yin taron sada zumunci a duk shekara.

Shugaban ƙungiyar, Ɗahiru Sa’id, yayin da ya ke jawabi a taron sada zumunci na bana, karo na 6 kenan, ya ce tallafin karatun wani ɓangare ne na taimakon da su ke bayarwa.

Ya ce “ƙungiyar ta samu nasarori da dama, da su ka haɗa da tallafin karatu na Naira miliyan 1 duk shekara ga ɗalibai ƴan asalin jihar Kano, marasa ƙarfi domin su samu damar biyan kuɗin makaranta.

“Haka kuma mu na tallafawa iyalan waɗanda su ka rasu a cikin mu. Mu na kuma fitar da ɗaurararru da ga gidajen yari da kuma kai ziyara zuwa gidajen marayu.

“mun kuma tallafawa waɗanda su ka samu ibtila’in ambaliyar ruwa, sannan mu na taimakawa marasa lafiya ƴan jihar Kano a asibitoci a faɗin jihar. Sannan kuma muna tallafawa junan mu idan ɗayan mu zai yi aure ko suna da sauran bukukuwa,” in ji Sa’id.

Ya kuma ƙara da cewa tun sanda a ka kafa ƙungiyar a 2016, ba ta taɓa gajiyawa wajen taimakon da yanke bayarwa ba, duk da halin da tattalin arziƙi ya faɗa sakamakon annobar korona.

Tun da fari dai ƙungiyar, a bisa jagorancin Farfesa Hajara Sanda, ta miƙa cekin naira miliyan 1 ga Shuagaban Jami’ar Bayero, Farfesa Sagir Adamu Abbas a ranar Juma’a.

Da ya ke jawabi bayan karɓar cekin kuɗin, Farfesa Abbas ya yabawa ƙungiyar, in da kuma yi kira ga sauran ƙungiyoyin tsoffin ɗalibai da su kwaikwayi irin aiyukan alherin da ƴan shekarar 1992 ɗin ke yi.

natforce latest news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Yunwa na kara tsananta a arewa maso gabashin Najeriya – ICRC

Kungiyar agaji ta Red cross (ICRC) ta bayyana yadda...

Ba zan taba watsawa Tinubu kasa a ido ba – IBB

Ɗan tsohon shugaban kasa, Janar Ibrahim Badamasi Babangida, wato...

Natasha kar ki kuskura ki dawo aiki – Majalisa

Majalisar Dattijai ta buƙaci Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta dakatar...

Za a yi ruwan sama da iska mai ƙarfi a jihohi harda Kano – NiMET

Hukumar kula da yanayi ta Najeriya (NiMET) ta fitar...

Obi da El-Rufa’i za su koma jam’iyyar mu a hukumance – ADC

Sakataren yada labarai na rikon kwarya na jam’iyyar African...

Za mu tattauna da tarayyar Turai a kan Nukiliyarmu – Iran

Iran ta tabbatar cewa za ta gudanar da tattaunawa...

Mu na gargadin Isra’ila kan korar al’ummar Gaza daga yankin su – MDD

Hukumar kula da ayyukan jin-ƙai ta Majalisar Ɗinkin Duniya...

Rikici ya kuma balle a Syria

Ƙungiyoyin kare haƙƙin dan'adam sun ce, wani sabon rikici...

Tsofaffin ‘Yansanda na da ‘yancin yin zanga-zanga – A Cewar Amnesty

Ƙungiyar Amnesty International ta ce tsofaffin ƴansandan Najeriya girmamawa...

Buhari ya yi wa Najeriya hidimar da ba za a manta da shi ba – António Guterres

Babban Sakatare na Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) António Guterres...

Binani ta koma jam’iyyar haɗaka ta ADC

'Yartakarar gwamnan jihar Adamawa a zaɓen 2023, Sanata Aishatu...

A Talata zan koma aiki na a majalisa – Natasha

Yar majalisar Dattawa, Sanata Natasha Akpoti, ta ci alwashin...
X whatsapp