fidelitybank

Tsaro: ‘Yan ta’adda sun aike da wasika ga mabioya addinin Kirista a Zamfara

Date:

Wasu gungun ‘yan bindiga sun rubuta wasika ga mabiya addinin Kirista a jihar Zamfara da ke Arewa Maso yammacin Najeriya cewa da su rufe coci-coci ko kuma su fuskanci munanan hare-hare.

A tattaunawa da Saharareporters, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Mohammed Shehu, ya ce ‘yan sanda sun san da wasikar barazanar, kuma suna kan gaba wajen shawo lamarin.

Ya ce, “Eh, zan iya tabbatar da cewa gaskiya ne, an aike da wasikar barazanar ga Kiristocin Jihar Zamfara su daina ibada da kuma rufe Coci. A gaskiya ‘yan sanda sun sanar da shugabannin addinin Kirista game da barazanar. Haka zalika kwamishina ‘yan sanda ya gayyaci shugabannin kungiyar Kiristocin Najeriya ta CAN a jihar, domin tattauna matakan tsaro a kan lamarin, dangane da haka, kwamishinan ya samar da wata tawaga ta musamman da za ta rika sintiri tare da kare masu ibada, musamman a ranar Lahadi. Bugu da ƙari, an tura ma’aikatan sanye da kayan aiki, domin tattara bayanan sirri da kuma bankado waɗanda ke da hannu a cikin wasikar barazanar,” in ji shi.

A ranar Lahadin da ta gabata ne wani daga cikin shugaban addinin Kirista da ya nemi a sakaya sunansa ya bukaci mabiya addinin Kirista a sassan duniya da su yi addu’a kan halin da suke ciki a Zamfara da sauran sassan Arewacin Najeriya.

 

 

vgn news 2022

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp