Kungiyar mafarauta ta Najeriya, ta yi alkawarin tallafa wa hukumomin tsaro, domin yaki da garkuwa da mutane, da fashi da makami, da sauran matsalolin rashin tsaro da kasar nan ke fuskanta a halin yanzu.
Shugaban kungiyar na kasa, Muhammadu Usman Baba Tola ya bayyana hakan a Bauchi a wajen taron shekara-shekara da kaddamar da sabbin jami’an kungiyar da a ka gudanar a dandalin Ibrahim Badamasi Babangida da ke Bauchi.
Ya ce, za a samu gagarumar nasara idan mafarauta da jami’an tsaro suka hada kai, domin cimma wata manufa guda.
Ya ce tabbatar da zaman lafiya a Najeriya shi ne babban abin da kowane mafarauci ke da shi a kasar, domin haka ya yi alkawarin cewa mafarauta a shirye suke su tunkari ‘yan bindiga da masu tayar da kayar baya a maboyarsu.
“Mafarauta sun san dazuzzuka da tsaunuka na Najeriya, za su iya taimakawa sosai ta wannan hanyar, mun hadu a Bauchi daga sassan Najeriya a yau domin sake duba al’amuran da su ka shafi kasa tare da sanin yadda za mu iya shigo da mu don taimakawa wajen magance wadannan matsalolin. mafi kyawun kasarmu,” inji Tola.
Ya bayyana cewa tuntubar gwamnati da sarakunan gargajiya da hukumomin tsaro na daga cikin hanyoyin da su ke bi.
Ya kuma jaddada cewa a shirye su ke su taimakawa masu ruwa da tsaki a harkar tsaro a kasar da nufin shawo kan matsalar rashin tsaro.
A nasa jawabin gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed ya yi alkawarin tallafawa mafarauta da gwamnatinsa za ta ba su damar gudanar da ayyukansu yadda ya kamata, domin kare rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar baki daya.
Gwamnan wanda ya samu wakilcin babban sakataren sa Sama’ila Burga, ya yaba da gudunmawar da mafarauta ke bayarwa wajen tabbatar da tsaro a jihar Bauchi tare da hadin gwiwar hukumomin tsaro na gwamnati.