Shahararren shugaban ‘yan ta’addan, Bello Turji, ya samu munanan raunuka a lokacin da jiragen yakin sojoji su ka kai farmaki maboyar sa da kuma sansanonin ‘yan bindiga a yankin Arewa maso Yamma.
PRNigeria ta rawaito cewa, harin da jiragen yakin rundunar sojin sama, ATF, Operation Hadarin Daji su ka kai, sun kuma kashe ‘yan ta’adda da dama, a wani samame da su ka kai a wasu dazuzzukan jihohin Zamfara da Sokoto, da sanyin safiyar Asabar.
Wata majiyar leken asiri ta soji ta bayyana cewa, farmakin da rundunar sojin sama ta kai tare da hadin gwiwar sojojin kasa na sojojin Najeriya, an kai harin ne a garin Shinkafi da ke Zamfara da Bafarawa da Isa a yankin Sabon Birni a jihar Sokoto.
A cewar majiyar leken asirin, ba a iya tantance ainihin adadin ‘yan ta’addan da aka kawar da su a hare-haren ta sama, a cikin aikin wayewar gari.
Sai dai rahotanni na nuni da cewa, wasu ‘yan ta’addan da su ka samu munanan raunuka sun yi yunkurin guduwa, amma dakarun kasa sun yi musu kwanton bauna.
Baya ga wani samame na kwatsam a Katsina da Zamfara, daga ranar 16 da 17 ga Disamba, 2021, jiragen NAF sun kai hare-hare a sansanonin ‘yan bindiga a yankin Isa, Sabon Birni da kuma Gabashin Tozei inda aka yi nasarar fatattakar ‘yan bindiga da dama yayin da wasu suka tsere cikin rudani.
Bugu da kari a safiyar ranar 18 ga watan Disamba, an kai hare-hare ta sama a kauyen Gebe da ke jihar Sokoto, inda har yanzu ‘yan bindigar suka ci zarafin jama’a da ba su ji ba gani ba. Amma duk da haka, kadan daga cikin ‘yan fashin ne suka tsere, suka bar makamansu, a cikin wannan tsar. Cewar majiyar inji majiyar.