fidelitybank

Tsaro: Ba ma iya barci da ido biyu ni da gwamna na – Sarkin Katsina

Date:

Mai martaba sarkin Katsina, Alhaji Abdulmuminu Kabir Usman, ya shaida wa mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, cewa da shi da gwamnan, Aminu Bello Masari, sam ba sa iya barci da ido biyu, saboda kalubalen tsaron da ya addabi jihar.

Sarkin ya bayyana hakan ne lokacin da yake jawabi ga mataimakin shugaban kasar, wanda ya kai masa ziyarar ta’aziyya, saboda rasuwar mahaifiyar attajirin nan, Alhaji Dahiru Mangal ranar Lahadi.

A cewarsa, “Wannan zuwan naka a karon farko tun da ka fara yakin neman zabe zuwa ne mai cike da tarihi a wajenmu. Yanzu a gida kake, kuma ka yi magana a kan matsalar tsaro, wadda ita ce babbar matsalar da ta dame mu. Ban jima da dawowa daga Kaduna ba, inda ina zuwa na iske kusan kiran waya 100 a kan wani shiri da ’yan ta’adda ke yi na kai hari, wanda a yanzu ya zama ruwan dare.

“Ni da Gwamna Masari, ba mu da wani lokacin da muke iya yin barci da idanunmu biyu a rufe, amma na yi matukar farin ciki da aka ayyana wadannan miyagun a matsayin ’yan ta’adda,” inji Sarkin.

Tun da farko dai a nasa jawabin, Farfesa Osinbajo ya ce, ya yi matukar murna da ya ji an ce yanayin tsaron jihar na dada inganta, kamar yadda Masari ya shaida masa.

“Shugaban Kasa ya tattauna da dukkan kwararru a sha’anin tsaro, kuma za a yi canji a inda ya kamata, domin a samu ingantuwar tsaro a fadin kasa”. A cewar Osibanjo kamar yadda Aminiya ta rawaito.

www.nigerianews.com

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp