Tsohon kwamashinan Ayyuka a jihar Kano, Mu’azu Magaji, wand aka fi sani da Ɗan-Sarauniya, ya musanta dukkan zarge-zargen da ake yi masa a gaban kotu, ciki har da zagin gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje.
A yau Litinin ne ake ci gaba da sauraron ƙarar wadda gwamnatin Kano ta shigar ta na zargin sa da ɓata sunan Ganduje da iyalansa a shafukan sada zumunta.
Bayan karanto masa tuhume-tuhumen da ake yi masa ne kuma tsohon kwamashinan ya musanta dukkaninsu.
Zarge-zargen sun hadar da zagin gwamna da ɓata sunan gwamna da yunƙurin tunzira al’umma wajen yin ƙarya a kan gwamna.
Lauyoyin Mu’azu Magaji ƙarƙashin jagorancin Barista, Ghazali Datti Ahmed, sun nemi a ba su belin wanda suke karewa.
Sai dai lauyoyin gwamnati ƙarƙashin jagorancin, Barista Wada Ahmad ke adawa da ƙudirin neman belin.
Ana ci gaba da tafka muhawara a gaban alƙali yanzu haka a majiyar BBC.