fidelitybank

Tsaro: Amurka da Rasha za su gana a kan Ukraine

Date:

Jami’an Amurka da na Rasha za su yi shawarwari kan harkokin tsaro a ranar 10 ga watan Janairu domin tattauna damuwarsu game da ayyukan sojan da su ke yi da kuma tunkarar tashin hankalin da a ke yi kan kasar Ukraine.

Mai magana da yawun gwamnatin Biden ne ya sanar da ranar da yammacin jiya Litinin, kuma ya ce akwai yiwuwar Rasha da NATO suma za su yi tattaunawa a ranar 12 ga watan Janairu, inda za a yi wani babban taro da suka hada da Moscow, Washington da sauran kasashen Turai a ranar 13 ga watan Janairu.

Mataimakin ministan harkokin wajen Rasha Sergei Ryabkov ya tabbatar da wadannan ranakun a jiya Talata, ya kuma ce yana fatan tattaunawar da Amurka za ta yi a Geneva za ta kaddamar da wani tsari da zai bai wa Moscow wani sabon garantin tsaro daga kasashen yammacin duniya.

Wannana matakin dai wani dogon buri ne na Moscow, wanda ya firgita kasashen Yamma ta hanyar tara dubunnan dakaru kusa da Ukraine cikin watanni biyun da suka gabata.

Ryabkov ya ce, za a gudanar da taron kungiyar tsaro ta NATO a ranar 12 ga watan Janairu a Brussels na kasar Belgium, yayin da tattaunawar ta ranar 13 ga wata za ta kunshi kungiyar tsaro da hadin gwiwa a Turai mai shelwata a Vienna, wadda ta hada da Amurka da kawayenta na NATO, da kuma Rasha da Ukraine da sauran tsoffin jihohin Soviet.

nnn news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp