Shugaba Bola Tinubu, ya isa birnin New York domin halartar taron babban zauren Majalisar Dinkin Duniya karo na 78.
Shugaban ya samu tarba daga ministan harkokin wajen Najeriya, Ambasada Yusuf Tuggar da Wakilin dindindin na Najeriya a Majalisar Dinkin Duniya, Farfesa Tijjani Muhammad-Bande da sauran jami’an gwamnati.
Taken babban taron na bana shi ne: ‘Sake gina amintaka da karfafa haÉ—in kai tsakanin Æ™asashen duniya da kuma haÉ“aka yunÆ™urin tabbatar da muradin Æ™arni.’
Tinubu zai kuma gabatar da jawabinsa na farko a ranar 19 ga watan Satumba.
Shugaban zai kuma shiga tattaunawa daban-daban kan batutuwan da suka hada da ci gaba mai dorewa da rigakafin annoba da ayyukan sauyin yanayi, da sake fasalin kudi na duniya a lokacin ziyarar tasa


 

 
 