Wakilin mazabar Abia ta Arewa a majalisar dattawa kuma tsohon gwamnan jihar Abia, Sanata Orji Uzor Kalu, ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta duba batun mayar da zaben kananan hukumomi zuwa hannun Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa INEC, maimakon maimakon Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Jiha.
Ya kuma ce, hakan zai kara karfafa ‘yancin cin gashin kan kananan hukumomi tare da rage matsin lamba ga gwamnatocin jihohi.
Orji Kalu ya kuma bukaci gwamnonin jihohin kasar nan da su amince da hukuncin a matsayin nasara ga dimokuradiyya.
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da mai shari’a Emmanuel Agim na kotun koli ya umurci gwamnatin tarayya da ta fara biyan kudaden kananan hukumomi kai tsaye zuwa asusunsun maimakon tura su zuwa hannun gwamnonin jihohin kasar nan.


