Shugaban kasa Bola Tinubu ya isa birnin Rio de Janeiro na Brazil domin halartar taron ƙungiyar ƙasashe ta Brics karo na 17.
Fadar shugaban ƙasa ta ce Shugaban Brazil Inacio Lula Da Silva ne ya gayyaci Tinubu taron na kwana biyu – a ranakun Lahadi da Litinin.
Ƙasashen da ke cikin ƙungiyar su ne Brazil, da Rasha, da Indiya, da China, da Afirka ta Kudu, yayin da Najeriya ta zama abokiyar hulɗar ƙungiyar a shekarar da ta gabata.
Mutanen da suka yi wa Tinubu rakiya sun haɗa da Ministan Harkokin Waje Yusuf Maitama Tuggar, da Gwamnan Binuwai Hyacinth Alia, da Gwamnan Neja Umaru Bago, da Gwamnan Legas Babajide Sanwo-Olu, da Gwamnan Delta Sheriff Oborevwori.