fidelitybank

Tinubu ya gamsu cewa zai iya lashe zaɓen Kano

Date:

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, a ranar Laraba a jihar Kano, ya bayyana fatansa na ganin jam’iyyarsa za ta lashe jihar Kano da Najeriya baki daya, a zaben 2023.

Tinubu, wanda al’ummar jihar suka yi masa gagarumin tarba, ya je Kano ne domin kaddamar da yakin neman zaben shugaban kasa na Arewa maso Yamma.

Ya godewa al’ummar jihar, bisa gagarumin fitowar da suka nuna, goyon baya da hadin kai.

Gwamna Abdullahi Ganduje ya yi kira ga magoya bayan jam’iyyar da su zabi APC tun daga sama har kasa a zabe mai zuwa.

Ya kuma tabbatar wa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC cewa kuri’un mutanen Kano na APC ne, inda ya ce jama’a sun ga ribar dimokuradiyya da gwamnatin APC ta samar.

Gwamnan ya ce jam’iyyar ta amince kuma ta samu kwarin guiwar dimbin jama’a da suka tarbi Asiwaju Bola Tinubu a Kano.

“Nasarar da aka samu taron bayyananne ne da kuma nuna fifikon mutanen Kano dangane da zabin da ke gabansu.

“Goyon bayan Gawun da Garo kuri’ar amincewa ce ga dan takarar gwamna da mataimakinsa,” NAN ta ruwaito cewa.

Ganduje ya ce, Tinubu yana da hali, iya aiki da kuma cancantar samar da shugabanci da kowa zai yi alfahari da shi a kasar nan.

legit.ng.news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp