fidelitybank

Tinubu ya fara sulhu tsakanin Ganduje da Shekarau

Date:

 

 

Yayin da rikicin jam’iya mai mulki, APC ya ƙi ci ya ƙi cinyewa a Jihar Kano, a na ta samun yunƙurin sasanta ɓangarorin da ke zaman doya da manja a jihar.

Bayan da kwamitin sulhu da APC ta kafa ya fara aiki a makon da ya gabata, inda ya yi iƙrarin cewa ya sulhunta tsakanin Gwamna mai ci, Abdullahi Ganduje da tsohon gwamna, Ibrahim Shekarau, alamu dai sun nuna cewa har yanzu a kwai sauran rina a kaba a game da dambarwar siyasar da ta dabaibaye jam’iyar a jihar.

Sai dai kuma, rahotanni sun nuna cewa, Jagoran APC na ƙasa, Bola Tinubu ya fara na shi yunƙurin na sasanta ɓangarori biyun a jam’iyar a Kano.

Daily Nigerian Hausa ta jiyo cewa a jiya Lahadi, Tinubu, wanda shine tsohon gwamnan Jihar Legas, ya gaiyaci Shekarau kuma sun haɗu a Legas ɗin domin sulhu tsakanin sa da abokin burmin sa, Ganduje.

Haka-zalika jaridar ta jiyo cewa shi ma Gandujen, Tinubu ya gaiyace shi, to amma ba ya ƙasar kuma da zarar ya dawo, to zai je Legas ɗin domin su tattauna da jagoran APC ɗin don shawo kan lamarin.

Tuni dai APC ta dare gida biyu a Kano, inda ɓangaren Ganduje da tsagin Shekarau ke iƙirarin cewa shine mai riƙe da shugabacin jam’iya.

A kwanannan ne dai wata babbar kotu a Abuja ta rushe shugabacin jam’iyar na jiha, ƙarƙashin Abdullahi Abbas na tsagin Ganduje, ta kuma tabbatar da Ahmadu Ɗanzago na ɓangaren Shekarau a matsayin shugaban APC a Kano.

 

 

 

 

 

cnn news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...

A sake sabon tsarin shugabancin INEC a Najeriya – Goodluck

Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, ya yi kira da...

Magoya bayan West Ham ku hada kai da Bowen – Potter

Mai horas da West Ham, Graham Potter ya bukaci...

Alhaki na ne kifewar jirgin kasa – Shugaban Hukumar

Shugaban hukumar jiragen ƙasa ta Najeriya (NRC), Kayode Opeifa,...
X whatsapp