Ezri Konsa ne ya zura kwallaye biyu a ragar Leicester City wanda ya baiwa Aston Villa damar komawa kan hanyar samun nasara karkashin sabon mai horaswar ta, Steven Gerrard, a karawar da suka yi a gasar Premier mako na 15.
Harvey Barnes ne ya fara zura kwallon farko a minti 14 wanda Leicester ta shiga gaban Aston Vila kafin su zare kwallo a zagayen farko.
Sai dai mai tsaron baya Konsa ya taba kwallon da Emi Buendia ya ci da kai kusan nan da nan kuma ya zura kwallo a raga da ya yi nasara sau uku a cikin wasanni hudu da ya yi, tun bayan da Gerrard ya zama sabon mai horaswar Aston Villa.