Gwamnatin tarayya ta ayyana gobe Talata, 15 ga watan Yulin shekarar 2025 a matsayin hutu domin jimamin rasuwar tsohon shugaban ƙasar Muhammadu Buhari.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da ma’aikatar harkokin cikin gida na ƙasar ta fitar, wanda babban sakataren ma’aikatar Magdalene Ajani ta sanya wa hannu, inda ta ce wannan ɗoriya ce kan sanar da kwana bakwai na jimamin rasuwar.
Ministan Harkokin Cikin Gidan ƙasar, Olubunmi Tunji-Ojo ne ya yi sanarwar a madadin shugaban ƙasar, Bola Tinubu.
Ministan ya ce ƙasar ta ayyana hutun ne domin nuna irin girmamawar da gwamnatin ke yi wa tsohon shugaban, da kuma godiya ga hidima da sadauwar da ya yi domin ciyar da ƙasar gaba.
“Muhammadu Buhari ya mulki Najeriya da gaskiya da amana da kuma matuƙar sadaukarwa musamman wajen haɗin kan Najeriya da cigabanta. Wannan hutun dama ne ga ƴan Najeriya domin tuna irin sadaukarwar da Buhari ya yi.”
Ya yi kira ga ƴan Najeriya su tuna mamacin ta hanyar koyi da shi wajen ɗabbaƙa zaman lafiya da son cigaban ƙasar da aka san marigayin da su.