fidelitybank

Teloli da masu sayar da kaya ku kiyaye sanya mutum-mutumi – Hisba

Date:

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta ce, har yanzu haramcin da ta sanya kan amfani da mutum-mutumi a shagunan sayar da kayan sa wa da na teloli a fadin Jihar na nan daram.

A watan Yunin bara ne dai hukumar ta sanar da haramta amfani da mutum-mutumin a Jihar, tare da barazanar kama duk wanda ya karya dokar.

A cewar Babban Kwamandan hukumar, Harun Ibn Sina, sun dauki matakin ne, saboda amfani da mutum-mutumin ya saba da koyarwar addinin Musulunci.

Sai dai a wani taro da ta yi da Kungiyar Teloli ta Kasa reshen Jihar ranar Alhamis, hukumar ta Hisbah ta sake jaddada cewa, haramcin na nan daram.

Hakan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sashen yada labarai na hukumar ya fitar a ranar Juma’a.

A cewar Ibn Sina yayin taron nasa da telolin “Hukumar Hisba ta Jihar Kano bisa dogaro da sashen dokar Hisba ta shekarar 2001, wacce aka yi wa kwaskwarima a 2003, ta hana kowanne mai dinki saka mutum-mutumi, wanda yake dauke da siffar mutum cikakkiya, ko ta mace ko ta namiji.

“Amma za a iya anfani da wanda babu kai ajikinsa ko a jikanta, ita ’yar tsanar da ake saka wa kaya.

“Wannan shine kadan daka cikin muhimman abin da aka tattauna a kai yau,” inji Ibn Sina.

Hukumar Hisbah ta bukaci Teloli da su bi dokar ta hukumar tare da neman su tsaftace sana’ar tasu.

sunnnewspaper

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp