fidelitybank

Tawagar Gwamnatin Kano ta shilla Saudiyya zuwa jana’izar Dantata

Date:

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya jagoranci wata babbar tawaga zuwa birnin Madina na Masarautar Saudiyya domin halartar jana’izar fitaccen ɗan kasuwa kuma dattijo, marigayi Alhaji Aminu Alhassan Dantata.

Gwamnan ya tashi daga filin jirgin sama na Malam Aminu Kano da daren Litinin, inda ya bayyana girmamawa da mutunta rayuwar marigayin a matsayin wani babban uba ga al’umma.

A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, Gwamna Abba Yusuf yana tare da Sarkin Kano, Khalifa Muhammadu Sanusi II da gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Umar Namadi, da tsohon gwamnan Jigawa, Barista Ali Sa’ad Birnin Kudu, da sauran manyan jami’an gwamnati da dattawan jihar Kano.

Marigayi Aminu Dantata, wanda ya shahara wajen kasuwanci da sadaka da hidimar jama’a, ya rasu ne a Abu Dhabi, babban birnin Hadaddiyar Daular Larabawa.

“Mutuwarsa ta bar giɓi a harkokin tattalin arziki da walwalar al’umma, tare da kammala wani babi mai muhimmanci a tarihin Najeriya.” in ji sanarwar.

Gwamnan yayin da yake zantawa da manema labarai kafin tafiyar, ya bayyana cewa marigayin yana da kyakkyawan tarihi na karamci da kishin jama’a wanda ya zarce ƙasashe da iyakoki.

“Halartar tawagar Kano a jana’izar alama ce ta matuƙar girmamawa da godiyar da al’ummar Kano ke da ita ga irin gudummawar da marigayin ya bayar a rayuwarsa.” sanarwar ta ƙara da cewa

legit news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Magoya bayan West Ham ku hada kai da Bowen – Potter

Mai horas da West Ham, Graham Potter ya bukaci...

Alhaki na ne kifewar jirgin kasa – Shugaban Hukumar

Shugaban hukumar jiragen ƙasa ta Najeriya (NRC), Kayode Opeifa,...

Tinubu ya haramta fitar da ɗanyen man kaɗanya

Shugaban kasa, Bola Tinubu, ya bayar da umarnin dakatar...

Hisba ta karɓi ƙorafe-ƙorafe 83,776 a Kano

Rundunar Hisbah ta jihar Kano ta bayyana cewa, a...

Ganduje ba dan cin hanci ba ne – Martanin Garba Ga Gwamnatin Kano

Tsohon kwamishinan yaɗa labarai na Jihar Kano, Muhammad Garba,...

Kungiyar Malaman Jami’o’i bangaren BUK sun yi zanga-zangar Lumana

Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU), reshen Jami’ar Bayero Kano (BUK),...

An gargadi Borno da Yobe da Jigawa su zama cikin shirin ambaliya

Akwai yiwuwar samun ambaliya a jihohin Borno, Jigawa da...

Kano na cikin jihohin da ba su yi katin zabe sosai ba – INEC

Bayanan da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Najeriya...

Mun gano filin wasa na Sani Abacha ba shi da inganci – NPFL

Hukumar shirya gasar cin kofin kwararru ta kasa (NPFL),...

Jirgin ƙasa daga Abuja zuwa Kaduna ya ya fadi

Jirgin ƙasa ɗauke da fasinjoji da ya taso daga...

Jami’in mu bai saci naira biliyan 6.5 ba – Gwamnatin Kano

Gwamnatin Jihar Kano ta karyata rahoton da ya zargi...
X whatsapp