fidelitybank

TASHIN HANKALI: An kama samari 3 su na dafa kan wata budurwa domin yin asirin samun kuɗi

Date:

An samu gagarumin tashin hankali a yankin Oke Aregba da ke Abeokuta, babban birnin Jihar Ogun, bayan da aka kama wasu samari su na dafa kan wata budurwa da aka ce budurwar ɗaya da ga cikinsu ce, domin yin asirin samun kudi.
A cewar rahoton Daily Post, da sanyin safiyar yau Asabar ne, wani mai suna Segun Adewusi, wanda shi jami’in tsaron al’umma ne, ya lura da yadda wasu yara maza huɗu su ke dafa wani abu da ake zargin kan mutum ne a wata tukunyar a gefen hanya.
Rahotanni sun baiyana cewa, nan take mai gadin ya sanar da ‘yan sandan da ke ofishin Adatan, inda suka je wurin da lamarin ya faru domin kama masu dafa kan, inda su ka cafke uku daga cikin yaran, ɗayan kuma ya tsere kafin ƴan sanda su zo wajen.
Wata majiya da ta tabbatar da faruwar lamarin, ta ce yarinyar da aka kashe mai suna Rofiat, mazauniyar Idi-Ape ce; ta kasance budurwa ga wani Soliu, wanda yanzu haka ya na komar ƴan sanda.
An ce Soliu ya yaudari yarinyar ne zuwa ɗakinsa, inda ya riƙe ta ya kuma buƙaci ɗaya da ga cikin abokansa ya yanka ta da wuka.
“Wadanda aka kama sun hada da Wriz Oladeinde mai shekaru 17 daga Kugba, Gafar Luukman mai shekaru 19 daga Kugba da Mustakeem Balogun daga Bode Olude, dukkansu a Abeokuta. Soliu shine saurayin yarinyar, ya gudu, amma daga baya aka kama shi.
“Sun kashe Rofiat, suka yanke mata kai, suka tattara gawar mara kai a cikin buhu sannan suka fara kona kan a tukunya. Sun gaya wa ’yan sanda a gaban taron jama’a cewa suna so su yi amfani da shi wajen asirin samun kuɗi.
“’Yan sanda sun tafi da gawar zuwa dakin ajiyar gawa,” wata majiya ta shaida wa wakilinmu ranar Asabar.
A cikin wani ikirari na faifan bidiyo, Mustakeem Balogun, ya ce, “Mun so mu yi amfani da kanta ne kawai don yin ibadar kudi. Soliu ya shake ta, ya ce in taimake shi, muka yanke mata kai.”
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Ogun, Abimbola Oyeyemi, ya tabbatar da faruwar lamarin.

vanguard 
nigeria

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp