Karamar Hukumar birni a Kano, ta fara tantance dalibai ‘yan asalin jihar, domin basu tallafin karatu.
Wata sanarwa da Malam Kamilu Sa’idu Bala, shugaban kwamitin tantancewar, ya sanya wa hannu a madadin shugaban ƙaramar hukumar, Faizu Alfindiki, ta bayyana cewa, an fara tantancewar na tsawon kwanaki 5 a ranar Alhamis din da ta gabata a ofishin ƙaramar hukumar ta birni.
Sanarwar ta bayyana cewa, tantancewar da aka tsara, zai gudana a karshen mako a tsakanin karfe 8:00 na safe zuwa 4:00 na yamma.
Sanarwar ta bukaci daliban da abin ya shafa da su ziyarci ofishin ƙaramar hukumar da katin shaida na makarantarsu.
Takardun shaidar dan asalin karamar hukumar.
Sauran abubuwan sun hada da, na asali shaidar shiga makaranta, rasit ɗin biya na ƙarshe.
Sanarwar ta kuma bukaci ƴan asalin ƙaramar hukumar wato ɗalibai da su yi amfani da damammaki, don haɓaka ayyukansu na ilimi


