fidelitybank

Tagwaye sun yi wa ƴar shekara 10 fyaɗe a Anambra

Date:

A na zargin wasu ƴan tagwaye, ƴan shekara 16 da haihuwa, Chukwuemeka da Chukwuebuka Okpe, da yiwa wata ƴar shekara 10 fyaɗe na taron dangi a Abagana, Ƙaramar Hukumar Njikoka ta Jihar Anambra.
Babbar Daraktar Gidauniyar Davina Care Foundation, Rachel Yohanna, ita ta shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa, NAN a yau Lahadi, a Awka, cewa mahaifiyar yarinyar, Benedict Sunday, wacce ma’aikaciyar jinya ce,  ta kawo karar.
NAN ta samu labarin cewa waɗanda ake zargin ƴaƴan mai kula da gidan da yarinyar ta ke zaune da iyayenta ne inda a ka ce ƴan tagwayen sun ci gaba da cin zarafin ta sabo da taki yarda da su yi mata fyaɗe a karo na biyu.
Yohanna ta ce an kai rahoton laifin a ofishin ‘yan sanda na Abagana a ranar 16 ga watan Janairu, kuma an kama wadanda ake zargin da mahaifiyarsu, Chinwe Okpe.
Ta ce an kai yarinyar zuwa cibiyar binciken laifukan fyaɗe ta Ntasi da ke babban asibitin Enugu-Ukwu, inda aka tabbatar da cewa an ci zarafin ta kamar yadda wasu gurare a gabanta da bayanta su ka nuna.
Ta kuma ce an kai yarinyar, tare da rakiyar dan sanda da wata innar ta zuwa gwaji na biyu a asibitin ‘yan sanda, yayin da mahaifiyar wadanda ake zargin ta ce sakamakon asibitin Ntasi na jabu ne.
A cewar Yohanna, da sakamakon gwaji na biyun ya fito, sai ya nuna cewa lallai an yi wa yarinyar fyaɗe.
 Yohanna ta ce a lokacin da ‘yan sanda ke yi mata tambayoyi, wadda abin ya shafa ta ce ‘yan tagwayen ne suka kai mata hari a bandaki yayin da mahaifiyarta ba ta nan, suka kwantar da ita a ƙasa su ka kuma yi mata fyaɗe.
“Yaran tagwayen har yanzu suna musanta cewa sun yi wa yarinyar fyaɗe,” in ji ta.
Yohanna ta ce yanzu haka yarinyar na ƙarƙashin kulawa yayin da aka mika karar zuwa sashin binciken manyan laifuka da leken asiri na  Akwa, domin ci gaba da bincike.
Ta ce za a gurfanar da tagwayen a gaban kotun shari’ar iyalai bayan bincike, yayin da gidauniyar za ta tattara tallafi da bin diddigin lamarin don tabbatar da cewa yarinyar ta samu taimakon jinya da kuma adalci,” inji ta.

sunnnewspaper

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...

A sake sabon tsarin shugabancin INEC a Najeriya – Goodluck

Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, ya yi kira da...

Magoya bayan West Ham ku hada kai da Bowen – Potter

Mai horas da West Ham, Graham Potter ya bukaci...

Alhaki na ne kifewar jirgin kasa – Shugaban Hukumar

Shugaban hukumar jiragen ƙasa ta Najeriya (NRC), Kayode Opeifa,...

Tinubu ya haramta fitar da ɗanyen man kaɗanya

Shugaban kasa, Bola Tinubu, ya bayar da umarnin dakatar...

Hisba ta karɓi ƙorafe-ƙorafe 83,776 a Kano

Rundunar Hisbah ta jihar Kano ta bayyana cewa, a...

Ganduje ba dan cin hanci ba ne – Martanin Garba Ga Gwamnatin Kano

Tsohon kwamishinan yaɗa labarai na Jihar Kano, Muhammad Garba,...

Kungiyar Malaman Jami’o’i bangaren BUK sun yi zanga-zangar Lumana

Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU), reshen Jami’ar Bayero Kano (BUK),...
X whatsapp