fidelitybank

Ta’addanci: Sojoji sun ragargaji yaran Turji a Sokoto

Date:

Rundunar Sojojin kasar nan sun kashe ’yan ta’adda da dama a musayar wuta da su ka yi da yaran dan bindigar nan, Bello Turji a Jihar Sokoto.

Yaran na Bello Turji sun gamu da ajalinsu ne a kauyukan Katanga da Satiru, bayan Babban da Kwamanda (GOC) na Runduna ta 8 ta Sojin kasa ta Najeriya ya jagoranci sojoji su ka shiga har kauyukan sun yi musu kofar rago a ranar Alhamis.

Aminiya ta rawaito cewa, wani dan sa-kai da ke tare da sojoji a lokacin harin ya ce, “A akalla motoci 20 ne su ka yi wa wurin dirar mikiya, mun dauki awanni mu na musayar wuta da su; In takaita maka bayani, har sai da jirgin yaki ya kawo dauki mu ka fatattake su suka ja baya. Zuwa yanzu da wuya a iya tantance yawan wadanda mu ka kashe, amma ba a kashe mana ko mutum daya ba. Mun samu nasara”.

Bayanan da Aminiya ta samu sun nuna cewa baya kauyukan Katanga da Satiru na hanun Turji da yaransa, suna cin karensu babu babbaka.

Wani mazaunin garin, Isa ya shaida cewa, a lokacin da a ke ba-ta-kashin, sun ga dandazon ’yan bindiga na zuwa wurin, domin marawa ’yan uwansu baya.

“Amma bayanan da muka samu sun nuna sun kwashi kashinsu a hannun sojoji; Yanzu haka GOC da dakarunsa na bin daji suna share ’yan bindigar a maboyansu”. A cewarsa.

Wata majiyar soji ta ce GOC din ya lashi takobi cewa ba zai kowa gida ba sai sun gama fatattakar ’yan bindiga daga yankin Gabashin Jihar Sakkwato.

“Jajirtacce ne kuma ba ya son duk abin da zai kawo nakasu, shi da kan shi ya ke jagorantar sojoji a daji,” inji majiyar.

vanguard (nigeria)

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp