fidelitybank

Sojoji sun ragargaji ƴan ta’adda a Kaduna

Date:

Rundunar sojoji ta kashe ‘yan fashin daji 11 a lokacin wata arangama da ‘yan fashin a yankin ƙaramar hukumar Birnin Gwari a jihar Kaduna.

A wata sanarwa da kwamishin tsaro da al’amuran cikin gida na jihar Samuel Aruwan, ya fitar ya ce a lokacin gumurzun dakarun sun yi arangama da ‘yan fashin dajin a ƙauyen Kakangi da katakaki.

Sanarwar ta ce, dakarun sun lalata sansanonin ‘yan fashin a garuruwan Bagoma da Rema da Bugai da Dagara da Sabon layi da Gagumi da Kakangi da katakaki da kuma Randagi.

Karanta Wannan: Ƴan bindiga sun sace mata biyu a jami’ar Tarayya ta Gusau

Aruwan ya ce, sojojin sun samu nasarar kashe ‘yan fashi 11 yayin da wasu da dama suka tsere da raunukan harbin bindiga.

Haka kuma sanarwar ta yi bayanin cewa a lokacin arangamar sojojin sun samu nasarar ƙwato bindigogi biyu ƙirar AK-47, da kwanson alburusan bindigogin biyu, sai alburusai 57 da babura shida.

Gwamnan jihar Malam Nasir El-rufai ya jinjina wa sojojin bisa wannan nasara, tare da kiransu da su ƙara ƙaimi wajen samun nasarar fatattakar ‘yan fashin daji a faɗin jihar.

latest nigeria news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Makami mai Linzami ya faɗa kan cibiyar tattara bayanan sirrin Isra’ila

Kafar yaɗa labarai ta gwamnatin Iran ta ce, ƙasar...

Iran ta ƙaddamar da sabbin hare-haren makamai masu linzami kan Isra’ila

Rundunar sojin Isra'ila ta ce, Iran ta ƙaddamar da...

Isra’ila ta na da makaman nukiliya 90

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya dade yana cewa Iran...

Kashe jagoran Iran Ayatullah shi ne kawo ƙarshen rikici – Isra’ila

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce duk wani shiri...

Jerin sunayen masu Fashin Waya 51 da aka kama a Kano

Rundunar ƴansandan Kano, ta fitar da jerin sunayen Mutane...

Iran ta dakatar da tashin jirgi a ƙasarta

Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Iran ta...

Poland za ta kwashe dukkannin ƴan ƙasarta daga Isra’ila

Poland na shirin kwashe kusan ‘yan kasarta 200 daga...

Kisan Binuwai abun haushi ne bai kamata a ƙyale ba – Atiku

Atiku Abubakar ya yi Allah-wadai da Kisan Benue, tare...

Ƴan Bindiga sun ajiye makamai a Katsina

Wasu fitattun jagororin ƴanbindiga da suka addabi yankunan ƙaramar...

Iran ta rataye Mutumin da ya yi mata leƙen asiri

Iran ta ce ta aiwatar da hukuncin kisa ga...

Isra’ila ta ci gaba da neman Mutanen da suka maƙale

Tawagar masu aikin ceto a Isra'ila na ci gaba...

Kotu ta bayar da umarni a kashe Matashi ɗan shekara 23 a Kano

Babbar kotun jihar Kano mai lamba 23 ƙarƙashin mai...
X whatsapp