Rundunar soji, ta ce, ta yi nasarar kubutar da wasu ‘yan makaranta mata hudu wadanda ‘yan Boko Haram suka sace.
Daya daga cikin matan ‘yan makarantar Chibok ce da aka sace shekaru takwas da suka wuce kuma an same ta da danta dan shekara hudu.
A ranar Juma’a ne sojojin suka kubutar da matan. Ba a sani ba ko sakin ‘yar makarantar Chibok din aka yi ko kuma kubutar da ita sojoji suka yi.
A watan Afrilun 2014 ne ‘yan Boko Haram suka sace dalibai a makarantar mata ta Chibok su 270 abin da ya harzuka ‘yan Najeriya har aka kiraye-kiraye a kan gwamnati ta yi kokarin kubutar da su.
Da yawa daga cikinsu dai sun kubuta yayin da wasunsu kuma aka musaya da su domin sakin wasu ‘yan kungiyar da gwamnati ta kama.


