DakarunĀ Operation Hadarin Daji (OPHD) a karkashin Operation Sahel Sanity II, sun kashe wasu masu tsatsauran ra’ayi guda biyu a jihar Zamfara.
Laftanar Suleiman Omale na OPHD ya fada a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar cewa “A ranar 16 ga Agusta, 2024, sojojin sun kashe ‘yan bindigar a yayin wani kazamin artabu a Unguwar Sarkin Musulmi a karamar hukumar Kaura Namoda.”
Ya ci gaba da bayanin cewa, bisa sahihan bayanan sirri, sojojin sun yi gaggawar mayar da martani kan rahotannin ayyukan ta’addanci a yankin, kuma da isar su, sai suka tsunduma cikin wani mummunan harin bindiga, inda suka yi nasarar kawar da biyu daga cikinsu.
A cewarsa, an tilastawa sauran āyan fashin janyewa cikin rudani yayin arangamar.
Laftanar Omale ya ci gaba da cewa, sojojin sun gudanar da wani samame, inda suka kwato babur guda daya na āyan taāaddar.
Ya yi nuni da cewa, tun daga lokacin an tabbatar da tsaro a yankin, tare da dakarun hadin gwiwa na Sector 1 (Arewa maso Yamma) Operation Hadarin Daji suna ci gaba da kai farmaki tare da gudanar da sintiri na karfafa gwiwa domin tabbatar da tsaron lafiyar alāummar yankin.


