fidelitybank

Sojoji sun kashe kasurgumin dan bindigan Kaduna

Date:

Rundunar Sojojin Saman Kasar nan. ta sanar da cewa ta kashe wani ƙasurgumin ɗan bindiga, Mustapha Abdullahi, da wasu yaransa guda biyar a Ƙaramar Hukumar Kaduna ta Arewa na Jihar Kaduna.

Daraktan watsa labarai da hulɗa da jama’a na rundurar, Edward Gabkwet ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, inda ya ce ɓangaren sojojin rundunar na musamman na 413 ne suka yi aikin.

Mista Gabkwet ya ce an tura sojojin ne bayan samun bayanan sirri a ranar 31 ga Agustan cewa ɗan bindigar tare da yaransa sun tunkari dajin Sabon Gida da ke kan hanyar Sabon Birni, inda ake tunanin sun nufa da zimmar garkuwa da mutane, ko cutarwar da wasu ko kashewa.

A cewarsa, ganin sojojin ke da wuya, sai ƴan bindigar suka buɗe wuta, wanda hakan ya sa sojojin suka mayar da martani har suka ci ƙarfinsu.

Sojojin sun samu nasarar kashe jagoran ƴan bindigar da yaransa, inda aka ƙwato bindigogin ƙirar gida da alburusai da wayoyoyi da layukan waya da sauransu.

“Muna cigaba da ƙoƙarin ganin mun fatattaki ƴan bindiga daga yankin Igabi da Birnin Gwari baki ɗaya.

“An kuma yaba wa ƙoƙarin sojojin tare da kira a gare su da ƙara ƙaimi a wannan aiki da suke yi na kare rayuwa da dukiyar al.umma,” inji shi.

legit nig. news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Ƴan Jagaliya sun caka wa Matashi kuwa lokacin da ya zo karɓar naman Sallah a Kano

Matashi Ibrahim Mahmud ya rasu sakamakon caka masa wuƙa...

Kallo Ya Koma Sama: Elon Musk zai fuskanci mummunar sakamako – Trump

Ana ci gaba da takun saka tsakanin shugaban Amurka...

Zulum ya miƙa kyautar Naira miliyan 100 ga iyalan Sojojin da aka kashe

Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno, ya bai...

Otal ɗin ƴan Najeriya ya kama da wuta wani ɓangaren a Saudiyya

Hukumar Alhazai ta Najeriya ta ce an samu tashin...

An kai hari maɓoyar Boko Haram a Borno

Biyo bayan sahihan bayanan sirri da aka samu, rundunar...

Alaƙar Trump da Elon Musk ta yi tsami sosai

Attajirin da ya fi kowa arziki a duniya, Elon...

An yi jana’izar Muhammad Uwais

An gudanar da jana'izar tsohon alkalin alkalan Najeriya, mai...

Musulman Nijeriya a cigaba da jajircewa – Obi

Ɗan takarar shugaban ƙasa a karkarshin jam'iyyar Labour a...

Akwai takaici ambaliyar Neja – IBB

Tsohon shugaban ƙasa, Janar Ibrahim Babangida, ya kwatanta ambaliyar...

Farfesa Jibril Aminu ya rasu ya na da shekaru 86

Allah ya yi wa Farfesa Jibril Aminu mai shekara...

Alhajin Najeriya ya rasu a tsayuwar Arfa

Wani Alhaji daga Najeriya ya rasu a filin Arfa...

Alhazai miliyan 1.673,230 ne ke gudanar da akin Hajji – GASTAT

Hukumar tattara alƙaluma ta Saudiyya (GASTAT) ta ce, Alhazai...
X whatsapp