Gamayyar Kungiyoyin Cigaban Matasa da Shugabannin Dalibai (CPYS) ta ce za ta marawa Asiwaju Bola Tinubu baya a matsayin dan takarar shugaban kasa a 2023 idan har ya goyi bayan fitowar sa.
Shugaban gamayyar kungiyoyin, Samuel Olalere, ya sanar da hakan a wani taron manema labarai a ranar Lahadi a Ikeja, Legas.
Ya ce kungiyar ta amince da kasancewar Tinubu da gogewa a matsayin wanda ya yi fice a cikin manyan da su ka cancanta a cikin masu neman kujerar shugaban kasa.
Ya ce,“Shugabanci, musamman a matakin shugaban kasa, galibi ba aikin fada da karfin jiki ba ne.
“Wannan shi ne dalilin da ya sa mu ka yi imanin cewa shugaban Najeriya a 2023 ya kamata ya kasance mutum ne da ya dace da shekarun da su ka dace, wanda ya tabbatar da cewa zai iya ganowa da kuma tura dimbin hazaka ga Najeriya domin ciyar da kasar gaba.”
“Mutumin da ya dace da wannan kudiri a hasashenmu shi ne Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, jagoran jam’iyyar APC na kasa,” inji Olalere.
A cewarsa, Tinubu ya mallaki hadakar kwarewa da kuma hanyar sadarwa da za ta bai wa Najeriya irin shugabancin da ya dace.
A jawabin sa ya ce“Ba zan yi watsi da muryoyin da ke kirana da in tsaya takarar shugabancin kasa a 2023 ba”. Inji Tinubu.
Sai dai ya ce dole ne Tinubu da jam’iyyar APC su daidaita tsakanin jagoran gwamnati da shugaban jam’iyyar ta hanyar baiwa matasa mukamin shugaban kasa.
Olalere ya ce dole ne jam’iyyar ta biya bukatun matasa a cikin shirye-shiryen siyasa na 2023 masu tasowa, domin samun daidaito na tsararraki a cikin daidaiton iko.