fidelitybank

Matsafi ya mutu a hannun ‘yan sanda

Date:

Wani matsafi mai suna, Alfa Tunde Olayiwola, wanda ke hannun ‘yan sanda a Akure da ke jihar Ondo bisa zargin mallakar wani kokon kan mutum ya fadi ya mutu a ranar Asabar.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan, DSP Olufunmilayo Odunlami, wanda ya tabbatar da mutuwar wanda a ke zargin a ranar Lahadin da ta gabata, ya musanta cewa ya na dukansa ko kuma gallaza masa har lahira.

Odunlami ya ce, wanda a ke zargin ya nuna bakon abu ne a yammacin ranar Asabar, inda a ka garzaya da shi asibiti inda daga baya a ka tabbatar da rasuwarsa.

“Ko a asibitin babu wani alamar cewa akwai wani duka a jikinsa; kuma ba a azabtar da shi ba.

“Ba za a iya azabtar da shi ba saboda gaskiyar abin da ke tattare da shi ya riga ya fito fili.

“Wadanda su ke wurin lokacin da a ka gabatar da Olayiwola a gaban manema labarai sun lura cewa ba a azabtar da shi ba,” inji Odunlami.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Ondo, Mista Oyeyemi Oyediran, ya gurfanar da Olayiwola a gaban manema labarai a ranar 23 ga watan Disamba a Akure tare da wasu mutane takwas da aka kama bisa laifuka daban-daban.

Oyediran ya bayyana haka ne cewa ana zargin Olayiwola da hannu wajen hada-hadar kudi kuma an kama shi ne a ranar 23 ga watan Disamba a Oka a cikin Garin Ondo.

“A ranar 23 ga watan Disamba da misalin karfe 9.20 na safe ‘yan sanda sun samu labarin cewa Alfa Tunde Olayiwola, na shirin karbar wani kaya da a ke zargin kokon kan mutum ne.

“Nan take ‘yan sanda suka dauki matakin, su ka kama malamin a Unguwar Ajagbale da ke Oka, cikin Garin Ondo.

“An samu wani sabon kokon kan mutum a hannun Olayiwola lokacin da a ka kama shi.

nigeria daily post

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Za mu ɗauki matakin hana sake faruwar kisan mutane – Gwamnatin Filato

Gwamnatin jihar Filato ta jaddada aniyarta ta ɗaukar mataki...

Babu barazanar tsaro a Abuja – Najeriya

Gwamnatin Tarayya ta ce, babu wata barazanar a babban...

Isra’ila za ta mayarwa da Iran martani duk da tsagaita wuta

Ministan tsaron Isra'ila, Katz ya bayyana cewa, ya ba...

Ba mu kai wa Isra’ila hari ba – Iran

Kafar watsa labarai ta Iran ta ruwaito gwamnatin ƙasar...

Duk da faduwar farashin mai NNPCL ya kara farashi

Kamfanin man fetur na Najeriya, NNPCL ya ƙara farashin...

Duk wasu ƙawayen Amurka za su ɗanɗanar kuɗarsu – Iran

Rundunar dakarun juyin juya halin Iran ta fitar da...

Iran ta mayar da martani kan sojojin Amurka dake Qatar

Kafofin yaɗa labaran Iran sun bayyana cewa ƙasar ta...

Faransa ba ta goyon bayan Amurka na kifer da gwamnatin Iran – Barrot

Ministan harkokin wajen Faransa ya ce, ƙasarsu ba ta...

Kotu a Kano ta ɗaure masu satar Yara

Babbar kotun jihar Kano da ke zamanta a Miller...

Ba wata hujja da Amurka za ta kai wa Iran hari – Rasha

An gudanar da tattaunawa tsakanin shugaban Rasha Vladimir Putin...

Tinubu ya miƙa saƙon ta’aziyya ga mutanen Kano da Kaduna da Borno

Shugaba Bola Tinubu ya yi Alla-wadai da kisan wasu...

Amurka ta tafka babban kuskure – Iran

Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi ya yi Alla-wadai...
X whatsapp