fidelitybank

Siyasa: PDP ce za ta lashe zaben 2023 – Nyesom Wike

Date:

Gwamnan Jihar Rivers, Nyesom Wike, ya ce, jam’iyyarsa ta PDP, za ta karbe kujerar shugaban kasa da a ke nema ruwa a jallo daga jam’iyya mai mulki ta APC a shekarar 2023 idan hukumar zabe mai zaman kanta ta ci gaba da tsarinta na gudanar da zabe ba tare da katsalandan ba.

Wike ya bayyana haka ne a ranar Litinin a wajen kaddamar da wasu ayyuka a jihar Rivers a lokacin bikin cikarsa shekaru 58 da haihuwa.

A halin yanzu dai jam’iyyar PDP ce ke rike da jihohi 13, yayin da jam’iyyar APGA ke da daya inda jam’iyyar APC ta mamaye sauran.

A ‘yan kwanakin nan ‘yan siyasan adawa da kungiyoyin farar hula sun yaba wa INEC kan bullo da tsare-tsare da ake amfani da su wajen tantancewa a lokacin zabe.

Da ya ke magana a ranar Litinin, Wike ya yabawa INEC a karkashin shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu, kan tsayawar da ta yi na nuna adawa da magudin zabe da kuma tsoratar da siyasa.

Gwamnan Ribas ya ce, “Da yardar Allah PDP za ta karbi mulki a 2023. Ina addu’ar INEC ta ci gaba da tsarin da ta bullo da shi, inda kowa zai je ya yi yakin neman zabe, kuri’ar mutane za ta kirga, domin idan kuri’un mutane za su kirgu. Yanzu masu rike da mukaman siyasa za su yi lissafi. Lokacin da kuri’un ku ba su kirga ba, masu rike da mukaman siyasa ba za su yi wa mutane hisabi ba”. Inji Wike.

vgn news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp