fidelitybank

Tsaro: Buhari ya yi iya bakin kokarin sa – Obasanjo

Date:

Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, ya ce jiran tsammanin da al’umma ke yi wa shugaba Muhammadu Buhari, sama da wanda ya ke yi a yanzu, daidai ya ke da jiran gawon shanu.

Obasanjo ya bayyana hakan ne ranar Litinin, yayin wani taro kan hanyoyin bunkasa tsaro da wata kungiya ta Global Peace Foundation and Vision Africa ta shirya a Abuja.

Ya ce, “Gaskiya daya ce, Buhari ya yi iya bakin kokarinsa, Idan mu ka ce sai ya yi sama da haka, to tabbas yaudarar kan mu mu ke yi. Ina mu ka dosa kenan? Ba zai yi wu mu zauna mu nade hannuwan mu ba kawai, na yi amanna wannan na daga cikin abubuwan da muke yi. Kuma ta yaya Najeriya za ta kasance bayan ya tafi? Addu’a ta ita ce Allah Ya ba shi tsawon rai ya kammala mulkin nan lafiya”.

Ya ci gaba da cewa, “Amma mai ya kamata mu yi wajen inganta yanayin da mu ke ciki a yanzu? Wannan nauyi ne da ya rataya a wuyan kowa baki daya”. A cewar Obasanjo.

Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, ya kuma ce, amfani da karfin soja kadai ba zai kawo karshen matsalar ta’addanci ba a Najeriya, dole sai an hada da wasu dabarun domin a tsira tare.

tribune newspaper

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Za mu ɗauki matakin hana sake faruwar kisan mutane – Gwamnatin Filato

Gwamnatin jihar Filato ta jaddada aniyarta ta ɗaukar mataki...

Babu barazanar tsaro a Abuja – Najeriya

Gwamnatin Tarayya ta ce, babu wata barazanar a babban...

Isra’ila za ta mayarwa da Iran martani duk da tsagaita wuta

Ministan tsaron Isra'ila, Katz ya bayyana cewa, ya ba...

Ba mu kai wa Isra’ila hari ba – Iran

Kafar watsa labarai ta Iran ta ruwaito gwamnatin ƙasar...

Duk da faduwar farashin mai NNPCL ya kara farashi

Kamfanin man fetur na Najeriya, NNPCL ya ƙara farashin...

Duk wasu ƙawayen Amurka za su ɗanɗanar kuɗarsu – Iran

Rundunar dakarun juyin juya halin Iran ta fitar da...

Iran ta mayar da martani kan sojojin Amurka dake Qatar

Kafofin yaɗa labaran Iran sun bayyana cewa ƙasar ta...

Faransa ba ta goyon bayan Amurka na kifer da gwamnatin Iran – Barrot

Ministan harkokin wajen Faransa ya ce, ƙasarsu ba ta...

Kotu a Kano ta ɗaure masu satar Yara

Babbar kotun jihar Kano da ke zamanta a Miller...

Ba wata hujja da Amurka za ta kai wa Iran hari – Rasha

An gudanar da tattaunawa tsakanin shugaban Rasha Vladimir Putin...

Tinubu ya miƙa saƙon ta’aziyya ga mutanen Kano da Kaduna da Borno

Shugaba Bola Tinubu ya yi Alla-wadai da kisan wasu...

Amurka ta tafka babban kuskure – Iran

Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi ya yi Alla-wadai...
X whatsapp